Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Nasirzadeh ya ce ma'aikatar tsaron kasar ce ta kera makamai masu linzami da aka harba a yakin kwanaki 12 wadanda aka kera ne a shekarun baya ne cen. Ya kara da cewa, "A yau, mun kera sabbin makamai masu linzami masu karfin gaske."
Ministan na Iran ya tabbatar da cewa za a yi amfani da sabbin makamai masu linzami idan Isra'ila ta sake kai hari kan kasarsa.
A ranar 13 ga watan Yuni, Isra'ila tare da goyon bayan Amurka, ta kai hari na kwanaki 12 kan Iran, inda ta kai hari kan wuraren soji da na nukiliya, da cibiyoyin farar hula, tare da kashe wasu daga shugabannin sojoji da masana kimiyyar nukiliya. Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan hedkwatar sojojin Isra'ila da na leken asiri da makami mai linzami da jirage marasa matuka da sauran cibiyoyin Isra'ila wanda ya haifar da munanan asarori.
Kai Hare-Hare Da Zarge-Zarge
A ranar 22 ga watan Yuni, Amurka ta kai hari kan cibiyoyin Iran tare da ikirarin kawo karshen shirinta na nukiliya. Tehran ta mayar da martani ta hanyar kai hari a sansanin Al-Udeid na Amurka da ke Qatar. Daga nan ne Washington taga ba dama ta ayyana tsagaita wuta tsakanin Tel Aviv da Tehran a ranar 24 ga watan Yuni.
Isra'ila da kawayenta, Amurka, na zargin Iran da neman kera makaman kare dangi, yayin da Tehran ta ce shirin nata an tsara shi ne da nufin zaman lafiya, ciki har da samar da wutar lantarki.
Kafin harin da Isra'ila ta kai kan Iran, Tehran da Washington sun yi shawarwari da dama a kaikaice dangane da shirin nukiliyar Iran.
Isra'ila ita ce kasa daya tilo a yankin da ke da makamin nukiliya, wanda ba ya karkashin kulawar kasashen duniya. Ta ci gaba da mamaye Falasdinu da yankuna a Syria da Lebanon tsawon shekaru da dama.
Your Comment